ASUU Ta Yabawa Majalisar Gudanarwar OOU Mai Barin Gado Kan Zaman Lafiya da Ci Gaban Jami’a
ASUU Ta Yabawa Majalisar Gudanarwar OOU Mai Barin Gado Kan Zaman Lafiya da Ci Gaban Jami’a
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Olabisi Onabanjo (OOU), ta yaba wa Majalisar Gudanarwar jami’ar mai barin gado ƙarƙashin jagorancin Farfesa Toyin Ashiru, bisa irin nasarorin da ta samu cikin shekaru huɗu da suka gabata.
Shugaban ASUU na reshen jami’ar, Dakta Ganiyu Yinusa, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar domin kammala wa’adin majalisar. Ya ce jami’ar ta samu zaman lafiya a fannin ƙwadago, ci gaba a harkokin ilimi, inganta jin daɗin ma’aikata da kuma mutunta tsarin gudanar da jami’a ba tare da katsalandan ba.
A cewarsa, Majalisar Gudanarwar ta samar da ingantaccen shugabanci tare da mutunta hurumin mahukuntan jami’a da Majalisar Dattawan Jami’a (Senate), lamarin da ya ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da inganta gudanarwa.
Yinusa ya kuma yaba da yadda aka aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU ba tare da yajin aiki ko wata takaddama ba, yana mai cewa hakan na daga cikin manyan nasarorin da majalisar ta bari a matsayin tarihi.
Har ila yau, ya jinjinawa Gwamnatin Jihar Ogun bisa samar da yanayin da ya bai wa jami’ar damar gudanar da ayyukanta cikin ‘yanci, ba tare da tsoma baki ba, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen ƙarfafa martabar jami’ar da bunƙasa ayyukan ilimi.
By
Umar Nusaiba Ibrahim
#NexViewTV #ASUU #OOU #OgunState #Education #HigherEducation #Nigeria #BreakingNews #University #AcademicExcellence

Comments
Post a Comment