Zargin $16bn: Ku Bincike Ni Idan Akwai Hujjar Na Yi Sata — Atiku Ga Tinubu
Zargin $16bn: Ku Bincike Ni Idan Akwai Hujjar Na Yi Sata — Atiku Ga Tinubu Umar Nusaiba Ibrahim Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta fito da kwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake masa na almundahana, maimakon ci gaba da maimaita tsoffin zarge-zarge. Atiku ya musanta cewa ya taɓa jagorantar aiwatar da aikin wutar lantarki da aka kashe dala biliyan 16, yana mai cewa Majalisar Tarayya ta taɓa binciken kwangilolin, amma ba a taɓa gayyatar sa domin ya amsa wani zargi ba. Ya ce a matsayinsa na Mataimakin Shugaban Ƙasa ya jagoranci kwamitin sayar da kadarorin gwamnati, amma ba shi ne ya jagoranci aiwatar da kwangilolin wutar lantarkin ba. Ya kuma musanta hannu a harkar gwanjon kamfanin Aluminium Smelter. Atiku ya ce idan akwai hujjar cewa ya wawure dukiyar ƙasa, gwamnati ta bincike shi, ta gayyace shi sannan ta gurfanar da shi a gaban kotu. Ya ce tun bayan da ya bar ofis a shekarar 2007, babu wata gwamnati da ...