Posts

NELFUND Ta Bayyana An Bai Wa Dalibai Lamunin Naira Biliyan 322

Image
  NELFUND Ta Bayyana An Bai Wa Dalibai Lamunin Naira Biliyan 322 Umar Nusaiba Ibrahim  Asusun Bayar da Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND, ya ce ya raba sama da Naira biliyan 322 a matsayin lamunin karatu ga dalibai tun fara shirin. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyer, ya bayyana hakan a Uyo yayin wani shirin wayar da kan jama’a kan tsarin lamunin, inda ya ce cibiyoyin ilimi 319 da sama da dalibai miliyan 1.6 ne suka amfana da shirin zuwa yanzu. Ya ce an samar da tsarin ne domin rage matsalolin kudi da ke hana daliban da suka cancanta samun damar ci gaba da karatunsu. A Jihar Akwa Ibom kuwa, NELFUND ta ce sama da dalibai 23,000 sun amfana, inda aka zuba kusan Naira biliyan 2.1 a jihar. Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya ce gwamnatin jihar na tallafa wa dalibai ta hanyar biyan kudaden karatu da bayar da tallafin karatu. Ya ce kwanan nan jihar ta fitar da Naira biliyan 1.3, tare da kara tallafin kowane dalibi daga Naira 20,000 zuwa Naira 50,000. Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar na ...

Zargin $16bn: Ku Bincike Ni Idan Akwai Hujjar Na Yi Sata — Atiku Ga Tinubu

Image
  Zargin $16bn: Ku Bincike Ni Idan Akwai Hujjar Na Yi Sata — Atiku Ga Tinubu Umar Nusaiba Ibrahim  Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta fito da kwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake masa na almundahana, maimakon ci gaba da maimaita tsoffin zarge-zarge. Atiku ya musanta cewa ya taɓa jagorantar aiwatar da aikin wutar lantarki da aka kashe dala biliyan 16, yana mai cewa Majalisar Tarayya ta taɓa binciken kwangilolin, amma ba a taɓa gayyatar sa domin ya amsa wani zargi ba. Ya ce a matsayinsa na Mataimakin Shugaban Ƙasa ya jagoranci kwamitin sayar da kadarorin gwamnati, amma ba shi ne ya jagoranci aiwatar da kwangilolin wutar lantarkin ba. Ya kuma musanta hannu a harkar gwanjon kamfanin Aluminium Smelter. Atiku ya ce idan akwai hujjar cewa ya wawure dukiyar ƙasa, gwamnati ta bincike shi, ta gayyace shi sannan ta gurfanar da shi a gaban kotu. Ya ce tun bayan da ya bar ofis a shekarar 2007, babu wata gwamnati da ...

Tinubu: Hausawa ginshiƙai ne na ci gaban Najeriya.

Image
  Tinubu: Hausawa ginshiƙai ne na ci gaban Najeriya. Daga: Ibrahim Sani Isyaku  Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana al’ummar Hausawa a matsayin manyan ginshiƙai da ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya da ci gabanta. Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙon 2da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, domin taya al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, wadda ake gudanar da bikin ta a fadar Mai Martaba Sarkin Daura da ke Katsina.  Shugaban ya kuma yaba da yadda harshen Hausa ya bunƙasa, yana mai cewa ya zama ɗaya daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su wajen haɗin kan al’umma da harkokin kasuwanci a sassa daban-daban na duniya. Tinubu ya taya ɗaukacin al’ummar Hausawa murnar wannan rana, tare da bayyana muhimmancin al’adun Hausa da harshen wajen haɗa kan jama’a. Ranar Hausa, wadda kuma ake kira Ranar Hausa ta Duniya, ana bikin ta a ranar 26 ga Agusta na kowace shekara. An fara ƙaddamar da ita ne a matsayin wani yunƙuri na ƙa...

Hukumar ICPC Ta Bankado Yadda Hukumar Da Ba Ta Da Tushe Ta Shiga Kasafin 2026

Image
 Hukumar ICPC Ta Bankado Yadda Hukumar Da Ba Ta Da Tushe Ta Shiga Kasafin 2026 Umar Nusaiba Ibrahim  Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta bayyana cewa an shigar da wata hukumar da ba ta da ingantaccen tushe na doka cikin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2026, ba tare da an tabbatar da sahihancin kafuwarta ba. Hukumar da ake kira PFIPC ta nemi a ware mata sama da Naira biliyan 3.85 domin biyan albashin ma’aikatanta. Daga bisani, an rage adadin zuwa Naira biliyan 1.3, wanda ya ƙunshi Naira miliyan 802 na albashi, Naira miliyan 200 na gudanar da ayyuka da kuma Naira miliyan 300 na manyan ayyuka. A rahotonta na bincike, ICPC ta ce Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya bai gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa ba domin tabbatar da sahihancin takardun da aka gabatar da su a matsayin hujjar kafa hukumar. Maimakon haka, an dogara da wasu lambobin gudanarwa da takardu daga Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya. Sai dai ICPC t...

FG Na Shirin Amfani Da Ribar Hannun Jari Da Ba A Karɓa Ba Wajen Tallafa Wa NELFUND

Image
  FG Na Shirin Amfani Da Ribar Hannun Jari Da Ba A Karɓa Ba Wajen Tallafa Wa NELFUND Umar Nusaiba Ibrahim  Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin amfani da wasu kuɗaɗen dividend da ba a karɓa ba, da kuma kuɗaɗen da ke cikin asusun dormant, wajen ƙarfafa Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma bayar da umarnin karkatar da kuɗaɗen da EFCC ta kwato, waɗanda babu wata shari’a ko wani cikas na doka a kansu, zuwa NELFUND domin tallafa wa shirin lamunin ɗalibai. Ministan Ilimi, Dr Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, inda ya ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da cewa NELFUND na da isasshen kuɗi kuma zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa yayin da yawan masu cin gajiyar shirin ke ƙaruwa. Alausa ya ce Attorney-General na Tarayya zai haɗa kai da Ministocin Ilimi da Kuɗi da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da cewa tsarin ya dace da doka. Ya kuma ce za a iya yin gyare-gyare ga dokokin da suka kafa asusun i...

Tinubu Na Taimakon Talakawa, Inji Gwamnan Sokoto

Image
  Tinubu Na Taimakon Talakawa, Inji Gwamnan Sokoto Umar Nusaiba Ibrahim  Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce ikirarin da ‘yan adawa ke yi na cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai kawo wani sauyi a rayuwar ‘yan Najeriya cikin shekaru uku ba, ba komai ba ne face farfaganda. Gwamnan ya ce tasirin manufofin gwamnatin Tinubu a rayuwar al’umma a bayyane yake. Ahmed Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin taron kasa na yini guda kan “Inganta Shigar Jama’a Cikin Siyasa da Adalcin Zamantakewa a Matsayin Mafita Ga Hadin Kan Kasa da Ci Gaba”, wanda kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya a Jos, Jihar Plateau. Gwamnan ya ce gwamnatin tarayya na samar da tallafin abinci da taki kyauta, tare da daukar wasu matakai domin rage radadin talakawa. Ya ce dukkanin abubuwan da gwamnatin Tinubu ta yi an rubuta su tare da adana bayanansu, yana mai cewa duk wanda bai ga tasirin shugaban kasar ba, kamar bai zauna a Najeriya ba. Gwamnan Sokoto ya kuma yi kira ga ‘...

FAAC: Gwamnonin Jihohi Na Fuskantar Tambayoyi Kan Yadda Suka Kashe N47.25tn Cikin Shekaru Uku

Image
  FAAC: Gwamnonin Jihohi Na Fuskantar Tambayoyi Kan Yadda Suka Kashe N47.25tn Cikin Shekaru Uku Umar Nusaiba Ibrahim  Gwamnonin jihohin Najeriya 36 na fuskantar ƙarin matsin lamba da tambayoyi kan yadda suka kashe kuɗaɗen da suka samu daga Asusun Tarayya, FAAC, bayan wani sabon rahoto ya nuna cewa gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba kusan N47.25 tiriliyan a cikin shekaru uku daga 2023 zuwa 2025. Bayanan da Ma’aikatar Kuɗin Najeriya ta fitar sun nuna cewa jimillar kuɗaɗen da matakan gwamnati uku suka samu daga FAAC tsakanin 2017 zuwa 2025 sun kai N93.13 tiriliyan. Sai dai sama da rabin wannan kuɗi, wato N47.25 tiriliyan, an raba shi ne a cikin shekaru uku bayan cire tallafin man fetur da wasu sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar. Adadin kuɗin da ake rabawa ya ƙaru sosai daga N10.09 tiriliyan a 2023, zuwa N15.26 tiriliyan a 2024, sannan ya kai sabon tarihi na N21.90 tiriliyan a 2025. Jihohi sun kasance cikin waɗanda suka fi ...