Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar da Sabon Kwamitin Yaƙi da Shaye-shaye da Daba
Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar da Sabon Kwamitin Yaƙi da Shaye-shaye da Daba
KANO, Najeriya – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da wani kwamitin haɗin gwiwa na hukumomi daban-daban domin ƙarfafa yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, daba da sauran ayyukan laifuffuka a faɗin jihar.
A yayin ƙaddamar da kwamitin, gwamnan ya kuma sanya hannu kan wani sabon umarnin zartarwa da zai ƙara ƙarfi ga matakan gwamnati na magance matsalar daba da sauran ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Gwamna Eng Abba ya bayyana cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan ƙalubalen da ke addabar matasan Kano, yana mai cewa matsalar na haddasa aikata laifuffuka, rushewar iyalai, tauye ci gaban tattalin arziki da kuma kawo cikas ga zaman lafiya.
Ya ce sabon kwamitin zai jagoranci dukkan matakan gwamnatin jihar na yaƙi da matsalar ta hanyar tattara bayanan sirri, aiwatar da doka, wayar da kan jama’a, gyaran halayen masu fama da shaye-shaye da kuma haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta samar wa kwamitin dukkan tallafin da yake buƙata, ciki har da kuɗaɗe, motocin aiki, ofisoshi, kayan aiki da kariyar tsaro, tare da ba shi cikakken ’yancin gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin gyaran masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, inda ya ce an riga an samar da cibiyoyi na musamman ga maza da mata domin kula da masu fama da wannan matsala.
A cewarsa, sabon umarnin zartarwar zai taimaka wajen tarwatsa ƙungiyoyin daba, rage rikice-rikicen siyasa masu ɗauke da tashin hankali da kuma ƙarfafa ayyukan hukumomin tsaro a jihar.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da kwamitin, shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewar da ya nuna masa da sauran mambobin kwamitin, tare da alƙawarin gudanar da aikin cikin gaskiya da ƙwazo.
A wani ci gaba kuma, Gwamna Eng Abba ya sake jaddada cewa Jihar Kano ta shirya tsaf domin kafa rundunar ’yan sandan jiha idan aka amince da tsarin a matakin ƙasa.
Ya bayyana cewa rundunar ba za ta maye gurbin ’Yan Sandan Najeriya ba, sai dai za ta yi aiki tare da su domin ƙara inganta tsaro da yaƙi da masu aikata laifuffuka a faɗin jihar.
#Kano #AbbaKabirYusuf #YakiDaShayeShaye #YakiDaDaba #Tsaro #MuhuyiMagajiRimingado #KanoState #Nigeria #NexViewNews

Comments
Post a Comment