Gwamnatin Tarayya Za Ta Tantance Gidaje Domin Gano Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tantance Gidaje Domin Gano Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta fara tantance gidaje a dukkan jihohin Najeriya da Babban Birnin Tarayya domin gano ainihin adadin yaran da ba sa zuwa makaranta, inda za ta yi amfani da tsarin da Jihar Kaduna ta ƙirƙira.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) za su gudanar da aikin domin tattara sahihan bayanai kan yaran, inda suke da kuma gidajen da suke zaune.
A cewarsa, wannan mataki zai maye gurbin ƙiyasin alkaluma da ingantattun bayanai, wanda zai taimaka wa gwamnati wajen tsara matakan da suka dace domin dawo da yaran makaranta.
Alausa ya yabawa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, bisa ƙaddamar da wannan tsari, yana mai cewa bayanan da aka tattara a Kaduna sun nuna adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya yi ƙasa da abin da aka yi hasashe a baya.
Shi ma Gwamna Uba Sani ya bayyana jin daɗinsa kan yadda gwamnatin tarayya ta amince da tsarin Kaduna, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta manufofin ilimi da ƙara yawan yaran da za su koma makaranta.
Hashtags:
#Education #OutOfSchoolChildren #Nigeria #FederalGovernment #Kaduna #TunjiAlausa #UbaSani #NBS #EducationReform #NexviewNews

Comments
Post a Comment