Ireland Ta Bai Wa Makarantun Firamare 19 da Laburaren Ƙasa Littattafai 1,300 a Lagos
Ireland Ta Bai Wa Makarantun Firamare 19 da Laburaren Ƙasa Littattafai 1,300 a Lagos
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Jakadan ƙasar Ireland a Najeriya, Peter Ryan, ya bai wa makarantu firamare na gwamnati 19 da Babban Laburaren Ƙasa na Najeriya da ke Legas littattafai 1,300 domin inganta al’adar karatu a tsakanin yara.
An raba littattafan ne ta hannun wakilinsa, Aduke Gomez, inda kowace makaranta da laburaren suka karɓi akwati ɗaya mai ɗauke da littattafai 65, waɗanda yawancinsu marubutan Najeriya ne suka rubuta.
Ryan ya ce shirin na nuna ƙudirin ƙasar Ireland na tallafa wa ilimi da bunƙasa al’adar karatu a Najeriya.
A nata ɓangaren, Shugabar Zaccheus Onumba Dibiaezue Memorial Libraries (ZODML), Ifeoma Esiri, ta buƙaci shugabannin makarantun da su yi amfani da wannan tallafi a matsayin tubalin gina cikakkun dakunan karatu.
Shugaban Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar Legas (LASUBEB), Hakeem Shittu, ya tabbatar da cewa za a kula da littattafan tare da amfani da su yadda ya kamata domin amfanin ɗalibai.
#Ireland #Lagos #Education #ReadingCulture #Books #PrimarySchools #Nigeria #LASUBEB #NationalLibrary #NexviewNews

Comments
Post a Comment