JAMI'A TA WANKE SHUGABANTA KAN ZARGIN BADAKALA


 

JAMI'A TA WANKE SHUGABANTA KAN ZARGIN BADAKALA


By

Umar Nusaiba Ibrahim


Mahukuntan Jami’ar Michael Okpara University of Agriculture, Umudike (MOUAU), sun bayyana cewa sabuwar Shugabar Jami’ar (Vice-Chancellor) dake jahar Abia,Farfesa Ursula Akanwa, ba ta da hannu a rikicin daukar ma’aikatan jami’ar da ya janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan.


Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a da Tsare-tsare na jami’ar, Mista Anyaso Anyaso, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata. Ya ce tun bayan da Farfesa Akanwa ta karɓi ragamar jagorancin jami’ar a ranar 1 ga Maris, 2026, ta sha bayyana wa al’ummar jami’ar cewa an riga an kammala aikin daukar ma’aikata tare da shigar da sunayen waɗanda aka ɗauka cikin tsarin biyan albashin gwamnati kafin ta hau mulki.


A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta ba jami’ar izinin daukar ma’aikata 426 ne kawai, kuma Majalisar Gudanarwar jami’ar ta amince da wannan adadi tare da umartar tsohuwar majalisar zartawar jami’ar da tabi wannan ka’ida.


Sai dai ya ce abin mamaki, an fitar da takardun ɗaukar aiki ga mutum 618, yayin da aka shigar da sunayen mutum 553 cikin tsarin Government Integrated Financial Management Information System (GIFMIS). Daga ƙarshe, tsarin ya amince da mutum 426 kacal, daidai da adadin da Gwamnatin Tarayya da Majalisar Gudanarwa suka sahalai.


Mr Anyaso ya kuma jaddada cewa Shugabar jami’ar ba ta da ikon shiga ko sauya bayanan da ke cikin tsarin GIFMIS, don haka ba za a ɗora mata alhakin cirewa ko karin Suna ga kowana ma’aikaci ba.


Ya yi kira ga jama’a da sauran masu ruwa da tsaki da su yi watsi da jita-jita da bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, ya kuma yi kira da ayi dogaro da sanarwar hukuma jami’ar kawai.


Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Anyaso ya musanta zargin cewa jami’ar ta yi amfani da ƙarfi wajen karɓe katunan shaidar ma’aikatan da aka cire daga aiki. Ya ce jami’ar ba ta bai wa waɗannan ma’aikata takardun korar aiki ba, kuma ba a tilasta musu mika katunan shaidarsu ba.


Majiyarmu ta shida mana cewa a ranar Litinin da ta gabata, wakilan ma’aikata 127 da aka cire daga aiki sun yi zargin cewa an wulaƙanta su yayin ƙoƙarin karɓe katunan shaidarsu, tare da cewa an maye gurbinsu da wasu sabbin ma’aikata.


Lamarin dai na ci gaba da janyo muhawara, yayin da mahukuntan jami’ar ke dagewa cewa sabuwar Shugabar jami’ar ba ta da hannu a dukkan zarge-zarge da akeyi kan wannan batu.


#NexViewTV

#MOUAU

#MichaelOkparaUniversity

#UniversityNews

#EducationNews

#HigherEducation

#NigeriaUniversities

#ViceChancellor

#Recruitment

#PublicStatement

#CampusNews

#NigeriaNews

#BreakingNews

#HausaNews

#NewsUpdate

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill