JAMI'AR ILORI TA KAWO MASLAHA KAN BATUN KUƊIN HAYA GA ƊALIBANTA
JAMI'AR ILORI TA KAWO MASLAHA KAN BATUN KUƊIN HAYA GA ƊALIBANTA
Jami’ar Ilorin (UNILORIN) ta tabbatar wa ɗalibai cewa za ta ci gaba da kare su daga tsadar kuɗin dakunan kwana. Hukumar jami’ar ta bayyana cewa ta yi watsi da buƙatar masu gidajen kwana masu zaman kansu ta ƙara kuɗin masauki da kusan kashi 100 cikin ɗari, kafin daga bisani a cimma yarjejeniya kan ƙarin kashi 30 cikin ɗari bayan tattaunawa.
Jami’ar ta ce gidajen da abin ya shafa mallakin masu zaman kansu ne, amma tana sa ido kan yadda ake gudanar da su domin kare muradun ɗalibai. Sabbin kuɗaɗen masaukin sun koma ₦255,000 na ɗakin mutum biyu, ₦234,000 na ɗakin mutum uku, da ₦204,000 na ɗakin mutum huɗu, tare da sharadin inganta gine-ginen da samar da ingantaccen wutar lantarki ciki har da amfani da hasken rana.
Ƙungiyar NANS reshen Jihar Kwara ta yabawa jami’ar bisa yadda ta gudanar da tattaunawar tare da fifita jin daɗin ɗalibai. Haka kuma ta buƙaci masu saka hannun jari su ƙara gina gidajen kwana domin rage matsalar masauki, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa tantance bayanai kafin wallafawa.
By
Nusaiba umar Ibrahim
#NEXVIEWTV #NEXVIEWNews #NEXVIEW #CallAndGist #NigeriaNews #BreakingNews #Education #UNILORIN #NANS #StudentWelfare

Comments
Post a Comment