Jami’ar Kogi Ta Samu Cibiyar Bincike Da Laburaren Dijital Na Zamani

 



Jami’ar Kogi Ta Samu Cibiyar Bincike Da Laburaren Dijital Na Zamani


By Umar Nusaiba Ibrahim 


An fara aikin gina Cibiyar Bincike ta Musamman (Research Centre of Excellence) da Laburaren Zamani na Dijital a Jami’ar Prince Abubakar Audu University. Babban Sakataren Financial Reporting Council of Nigeria, Dakta Rabiu Olowo, ne ya ɗauki nauyin wannan aiki domin inganta bincike da ilimi a jami’ar da ya yi karatu.


Mai kula da aikin, Dakta Mohammed Umar, ya bayyana cewa za a gina cibiyar ne bisa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, inda za ta ƙunshi laburaren dijital mai ɗauke da dimbin littattafai da bayanan ilimi da ɗalibai, musamman masu karatun lissafin kuɗi (Accounting), za su iya amfani da su daga jami’o’i daban-daban.


Ya ƙara da cewa cibiyar za ta yi haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙwararru na cikin gida da na ƙasashen waje domin samar da littattafan dijital kyauta, tare da bai wa malamai damar samun sabbin wallafe-wallafen bincike. Haka kuma za ta taimaka wajen samo tallafin kuɗaɗe domin gudanar da bincike a jami’ar da sauran manyan makarantu.


A cewarsa, cibiyar za ta kasance da wutar lantarki mai ɗorewa, intanet mai sauri, rijiyar burtsatse da dakunan taro na zamani domin samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa. Ya ce Dakta Rabiu Olowo ya ƙaddamar da wannan aiki ne saboda kishinsa na bunƙasa ilimi, bincike da ƙirƙire-ƙirƙire a jami’ar da ma Najeriya baki ɗaya.


#Kogi #PAAU #Education #Research #DigitalLibrary #Nigeria #LabaranYau #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill