Jihar Yobe Ta Fara Cikakken Aiwatar da Yarjejeniyar 2025 da ASUU
Jihar Yobe Ta Fara Cikakken Aiwatar da Yarjejeniyar 2025 da ASUU
DAMATURU – Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Yobe, Farfesa Muhammad Tahir, ya bayyana cewa Gwamna Mai Mala Buni ya amince da cikakken aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), tare da biyan dukkan bashin alawus da albashin da ake bin malaman jami’ar.
A cewarsa, matakin zai inganta jin daɗin ma’aikata, ƙarfafa koyarwa da bincike, bunƙasa kirkire-kirkire tare da haɓaka ingancin aiki a jami’o’in gwamnatin jihar Yobe. Ya kuma yabawa gwamnatin Buni bisa ci gaba da ba ilimi muhimmanci ta hanyar zuba jari a fannin gine-gine, horar da ma’aikata da tallafawa bincike.
Idan ba'a mantaba da a watan jiya mun labarta muku cewa an shiga zaman tankiya tsakanin ƙungiyar ASUU da gwamnatin jihar yobe kan batun shiga yajin aiki kan wannan batu
Sai dai ASUU ta ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da yarjejeniyar gaba ɗaya ba, tana mai cewa har yanzu ana bin malamai a jami’o’in tarayya da na wasu jihohi bashin albashi da sauran haƙƙoƙinsu.
#NexviewTV #YobeState #MaiMalaBuni #ASUU #Education #NigeriaNews #Jamia #Ilimi

Comments
Post a Comment