Majalisar Dokokin Kano Za Ta Binciki Tsadar Kuɗin Dillalan Gidaje da Masu Gidajen Haya
Majalisar Dokokin Kano Za Ta Binciki Tsadar Kuɗin Dillalan Gidaje da Masu Gidajen Haya
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta kaddamar da bincike kan zargin da ake yi wa dillalan gidaje da masu gidajen haya na tsawwala wa al’umma kuɗaɗen haya da sauran caji.
Matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da mazauna jihar suka gabatar, inda suka bayyana cewa ƙarin kuɗaɗen na ƙara jefa mutane cikin wahalar samun gidaje da filaye.
Sakataren Yaɗa Labaran Majalisar, Kamalu Sani Shawai, ya ce Majalisar za ta yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin gudanar da cikakken bincike. Ya kuma bayyana cewa za a duba yiwuwar sake nazarin dokar da ke tsara ayyukan dillalan gidaje, domin samar da mafita ga matsalar tare da kare muradun al’umma.
#MajalisarKano #KanoState #Gidaje #MasuGidajenHaya #DillalanGidaje #Housing #KanoNews #NexViewNews #NigeriaNews

Comments
Post a Comment