NABTEB ta fara tantancewa da raba ɗalibai zuwa kwalejojin fasaha a faɗin Najeriya
NABTEB ta fara tantancewa da raba ɗalibai zuwa kwalejojin fasaha a faɗin Najeriya
By
Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Shirya Jarabawar Kasuwanci da Fasaha ta Ƙasa (NABTEB) ta sanar da fara aikin zaɓe da raba ɗaliban da suka cancanta zuwa kwalejojin fasaha na tarayya da na jihohi a faɗin ƙasar nan bayan kammala jarabawar shiga ta shekarar 2026.
Magatakardar kuma Babban Jami’in Hukumar, Dakta Mohammed Aminu, ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja, inda ya ce wannan mataki na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa an ba wa waɗanda suka cancanta guraben karatu cikin adalci, gaskiya da bin ƙa’idojin da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta gindaya.
A cewarsa, mutum 15,290 ne suka yi rajistar jarabawar shiga kwalejojin fasaha ta bana, amma mutum 13,848 ne suka rubuta jarabawar. Daga cikinsu, mutum 10,426, wato kashi 75.29 cikin ɗari, sun samu maki 50 cikin ɗari ko sama da haka, yayin da mutum 5,708, daidai da kashi 41.22 cikin ɗari, suka samu maki 70 cikin ɗari ko fiye.
Dakta Aminu ya ce za a gudanar da zaɓen ɗaliban ne bisa cancanta, adalci, gaskiya, riƙon amana da kuma bin tsarin Federal Character domin tabbatar da cewa kowace jiha ta samu wakilci yadda ya kamata. Ya kuma buƙaci mambobin kwamitin zaɓen su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rashin son kai.
Ya ƙara da cewa NABTEB ta samu ci gaba wajen gudanar da jarabawar bana ta hanyar amfani da tsarin jarabawar kwamfuta (CBT), inganta fitar da sakamako ta hanyar fasaha da kuma amfani da tsarin basirar wucin gadi (AI) wajen tantance irin kwas ɗin da ya dace da kowane ɗalibi. A cewarsa, hakan zai ƙara inganta inganci da gaskiya a tsarin ɗaukar ɗalibai.
Magatakardar ya jaddada cewa kwalejojin fasaha ba wuraren da ake tura waɗanda suka gaza ba ne, illa cibiyoyi ne da ke horar da matasa kan sana’o’i, ƙwarewar hannu, kirkire-kirkire da kasuwanci domin su zama ƙwararrun ma’aikata da za su taimaka wajen bunƙasa masana’antu da tattalin arzikin Najeriya.
Haka kuma ya yaba wa Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, bisa sauye-sauyen da yake jagoranta domin bunƙasa ilimin sana’o’i da fasaha, ciki har da ƙara zuba jari a fannin koyon sana’o’i, haɗin gwiwa da masana’antu da kuma amfani da fasahar zamani.
Ya yi kira ga gwamnatoci, shugabannin makarantu, iyaye, al’ummomi da ƙungiyoyin ci gaba da su ƙara wayar da kan matasa kan muhimmancin ilimin sana’a da fasaha domin rage rashin aikin yi da samar da ƙwararrun ma’aikata da ƙasar ke buƙata.
#GaLabaranMuNaYau
#NABTEB
#TechnicalEducation
#TVETNigeria
#EducationNigeria
#SkillDevelopment
#VocationalEducation
#NigeriaEducation
#YouthEmpowerment
#NewsUpdate

Comments
Post a Comment