NERDC Ta Rage Kuɗin Tantance Littattafai Da Kashi 25 Cikin 100
NERDC Ta Rage Kuɗin Tantance Littattafai Da Kashi 25 Cikin 100
By
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin tantancewa da tsarin ƙimar littattafan karatu ta hannun Hukumar Bincike da Bunƙasa Manhajar Ilimi ta Ƙasa (NERDC), tare da umartar a mayar wa masu buga littattafan da suka biya tsohon kuɗin tantancewa ragowar kuɗinsu.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Hukumar NERDC, Prof. Salisu Shehu, ya sanya wa hannu, wadda aka fitar a ranar Laraba a Abuja.
Sabon tsarin ya rage kuɗin tantance kowane shafi daga Naira 2,000 zuwa Naira 1,500, yayin da kuɗin tsarin ƙima (ranking) na kowane taken littafi ya sauka daga Naira miliyan 1 zuwa Naira 750,000.
A cewar Prof. Shehu, sabon tsarin ya fara aiki nan take, kuma an ƙaddamar da shi ne domin rage wa masu buga littattafai da marubuta nauyin kuɗi yayin da ake shirin fara aiwatar da sabon tsarin tantance littattafai na ƙasa.
Hukumar ta kuma bayyana cewa duk masu buga littattafan da suka riga suka biya tsohon kuɗin tantancewa za a mayar musu da abin da ya zarce sabon farashin, yayin da za a sanar da yadda za a aiwatar da mayar da kuɗin nan ba da jimawa ba.
NERDC ta buƙaci masu buga littattafai, marubuta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wallafe-wallafe su bi sabon tsarin kuɗaɗen da aka ayyana.
Wannan mataki na zuwa ne gabanin fara aiwatar da National Textbook Ranking System daga watan Satumban 2026, wani babban sauyi da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaddamar domin inganta ingancin littattafan karatu da ake amfani da su a makarantun Najeriya.
A ƙarƙashin sabon tsarin, littattafan da ba su samu tantancewa, amincewa da kuma ƙima daga NERDC ba, ba za a amince da amfani da su a azuzuwan makarantu ba.
Gwamnatin Tarayya ta ce manufar wannan shiri ita ce kawar da ƙarancin ingancin littattafan karatu, ƙarfafa tsarin tabbatar da inganci, da kuma tabbatar da cewa ɗalibai da malamai suna amfani ne kawai da littattafan da suka dace da manhajar karatu ta ƙasa.
#FG #NERDC #Education #TextbookRanking #NigeriaEducation #SchoolBooks #Curriculum #NexViewNews

Comments
Post a Comment