Wani Alƙalin Kotun Shari'a Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Harin 'Yan Bindiga A Cikin Kotu


 

Wani Alƙalin Kotun Shari'a Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Harin 'Yan Bindiga A Cikin Kotu


Kabir Garba Hassan 



Alƙalin Kotun Shari'ar muslunci da ke ƙauyen Gwarjo a Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina, Malam Mohammed Muktar, ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari har cikin harabar kotun a ranar Laraba.


Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da tsakar rana lokacin da maharan suka kutsa cikin kotun suna harbe-harbe tare da neman a nuna musu inda alƙalin yake.


Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa alƙalin ya hango maharan tun kafin su iso kotun, lamarin da ya ba shi damar tserewa ta taga kafin su shiga cikin ɗakin shari'a.


Wani mazaunin yankin ya ce bayan shiga kotun, 'yan bindigar sun ci gaba da harbe-harbe suna tambayar inda alƙalin yake. Sai dai ya ce wani direban babur ya taimaka masa wajen ficewa daga yankin cikin gaggawa kafin maharan su same shi.


Wani shaidar gani da ido ya kuma bayyana cewa maharan sun fusata bayan sun fahimci alƙalin ya tsere, inda suka yi barazanar kashe shi idan ya sake dawowa domin gudanar da zaman kotu a ƙauyen.


Wannan hari ya ƙara tayar da hankalin mazauna Gwarjo, yankin da ya sha fama da hare-haren 'yan bindiga a lokuta daban-daban.


Ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aika masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


#Katsina

#Matazu

#Gwarjo

#KotunShari’a

#Alkali

#YanBindiga

#Tsaro

#LabaranKatsina

#LabaranHausa

#NigeriaNews

#BreakingNews

#Insecurity

#Justice

#NexviewTV

#ArewaNews

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill