2027: Atiku Ya Yi Alƙawarin Dawo Da Tallafin Man Fetur
2027: Atiku Ya Yi Alƙawarin Dawo Da Tallafin Man Fetur
Umar Nusaiba Ibrahim
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da DCL Hausa, inda ya ce ba ya adawa da cire tallafin man fetur, sai dai yana tambayar yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da gwamnati ta samu bayan cire tallafin. Ya ce ya kamata a yi amfani da kuɗaɗen wajen rage talauci da inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen amfani da kuɗaɗen gwamnati yadda ya kamata, tare da ikirarin cewa ana karkatar da dukiyar ƙasa. Atiku ya ce idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar, zai tabbatar da cewa duk wanda ya wawure kuɗin gwamnati ya dawo da su.
Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur jim kaɗan bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, lamarin da ya haifar da tashin farashin man fetur da ƙarin tsadar rayuwa. Gwamnatin Tinubu ta sha kare matakin, tana mai cewa cire tallafin ya rage nauyin da gwamnati ke fuskanta.
Atiku ya ce manufarsa ita ce tabbatar da cewa dukiyar ƙasa tana amfanar jama’a, yana mai cewa ’yan Najeriya bai kamata su ci gaba da fuskantar matsanancin hali ba. Dawo da tallafin man fetur na daga cikin muhimman manufofin da ya bayyana gabanin zaɓen 2027.
#AtikuAbubakar #Zaben2027 #TallafinManFetur #Nigeria #Tinubu #ADC #SiyasarNigeria #TattalinArziki #ManFetur #NigerianPolitics

Comments
Post a Comment