2027: Malaman Tsangaya a Gombe Sun Yi Wa Jamilu Gwamna Alƙawarin Ƙuri’u 150,000
2027: Malaman Tsangaya a Gombe Sun Yi Wa Jamilu Gwamna Alƙawarin Ƙuri’u 150,000
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Malaman Tsangaya da malaman addinin Musulunci a jihar Gombe sun bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Jamilu Isyaku Gwamna, tare da alƙawarin samo masa ƙuri’u 150,000 a zaɓen 2027.
Malaman sun bayyana hakan ne a wani taro da ya tattaro wakilan malaman Tsangaya da na addini daga mazaɓu 114 da ke cikin ƙananan hukumomi 11 na jihar.
Sun ce matakin na su ya samo asali ne daga ayyukan gwamnatin Gombe na inganta tsarin karatun Tsangaya, ciki har da gina makarantu 11, samar da cibiyoyin karatu sama da 120, da kuma ba ɗalibai damar koyon sana’o’i domin dogaro da kai.
Haka kuma, malaman sun yaba da shigar da almajirai 1,000 cikin tsarin inshorar lafiya na jihar, tare da kafa Hukumar Almajiri da za ta kula da harkokin ilimin Alƙur’ani da ci gaban yaran da ke karatun Tsangaya.
Goni Chashiya, wanda ya yi jawabi a wajen taron, ya ce manufar taron ita ce nuna godiya ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta ilimin addini. Ya ce sun yarda da Jamilu Gwamna ne saboda ganin cewa zai iya ci gaba da manufofin da ake bi a yanzu.
A nasa bangaren, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Gombe, Abubakar Inuwa Kari, ya ce gwamnatin jihar na kokarin tabbatar da cewa manufofi da ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa sun samu dorewa ta hanyar ingantaccen tsarin mika mulki.
#Gombe #JamiluGwamna #APC #2027Election #MalamanTsangaya #Tsangaya #GombePolitics #NigeriaPolitics #Zabe2027 #GwamnatinGombe

Comments
Post a Comment