2027: ’Yan Sandan Kano Sun Gargadi ’Yan Siyasa Kan Amfani da Daba
2027: ’Yan Sandan Kano Sun Gargadi ’Yan Siyasa Kan Amfani da Daba
Umar Nusaiba Ibrahim
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi ’yan siyasa, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji amfani da ’yan daba wajen gudanar da harkokin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Kwamishinan ya kuma ja kunnen ’yan siyasa kan yaɗa kalaman ƙiyayya, labaran ƙarya da kuma duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali a jihar, musamman a kafafen sada zumunta.
Bakori ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Alhamis, 28 ga Agusta, 2026, yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa da ’yan takara a jihar Kano, wadda aka gudanar a hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Bompai.
Ya ce taron na da nufin tabbatar da cewa harkokin siyasa da za su kai ga zaɓen 2027 sun gudana cikin lumana tare da mutunta doka. Ya kuma bayyana cewa girman Kano da muhimmancinta a siyasar Najeriya na buƙatar ’yan siyasa su yi taka-tsantsan wajen gudanar da kamfen da sauran ayyukan siyasa.
Kwamishinan ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci tashin hankali ko amfani da daba ba, tare da yin barazanar kama da gurfanar da duk wanda ya karya dokar zaɓe ko ya kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.
Ya kuma buƙaci jam’iyyu da ’yan takara su tabbatar da bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2022 da ƙa’idojin INEC, ciki har da neman izinin gudanar da gangami da sauran tarukan siyasa.
A wani labarin kuma, rundunar ’yan sandan Kano ta sanar da kama wani da ake zargi da safarar makamai a ƙaramar hukumar Dala. Rundunar ta ce ta ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da harsasai, tare da wasu makamai.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa ya samo makaman ne daga jihar Katsina, kuma ana ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a safarar makaman.
#Kano #KanoPolice #2027Election #SiyasarKano #YanDaba #Tsaro #Zaben2027 #INEC #DokarZabe #Nigeria #KanoState

Comments
Post a Comment