ABU Ta Fara Binciken Takardun Karatun Farfesa Abdullahi Abubakar
ABU Ta Fara Binciken Takardun Karatun Farfesa Abdullahi Abubakar
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) ta fara bincike kan sahihancin takardun karatun wani farfesa a jami’ar, Arc. Abdullahi Abubakar, bayan wasu bayanai da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun jawo ce-ce-ku-ce.
Rahotannin da suka yaɗu sun nuna cewa farfesan na da digirin PhD guda biyar, digirin Master guda biyar, digirin farko guda bakwai da difloma 11, lamarin da ya jawo hankalin jama’a.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na ABU, Awwal Umar, ya tabbatar da cewa jami’ar na sane da batun, tana kuma gudanar da binciken da ya dace domin tabbatar da sahihancin bayanan.
Ya ce ABU ba za ta yi gaggawar yanke hukunci ba, inda ta bayyana cewa za ta sanar da matsayinta a hukumance bayan kammala binciken da kuma tabbatar da sahihan bayanai.
A nasa bangaren, Farfesa Abdullahi Abubakar bai amsa kiran waya da aka yi masa ba, amma ya tabbatar da samun saƙon neman jin ta bakinsa, inda ya ce ba zai yi tsokaci kan batun a yanzu ba.
#AhmaduBelloUniversity #FarfesaAbdullahiAbubakar #Bincike #TakardunKaratu #Ilimi #JamiA #Nigeria #NexviewTV

Comments
Post a Comment