Accord Party ta zargi APC da ɓoye masu kutse a Osogbo


 

Accord Party ta zargi APC da ɓoye masu kutse a Osogbo


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Jam’iyyar Accord Party a jihar Osun ta zargi jam’iyyar APC da kawo wasu masu kutse a tsarin kwamfuta daga Legas da Abuja, tare da zargin cewa an ajiye su a wani otal da ke Osogbo domin kutse cikin tsarin hukumar zaɓe ta INEC.


Shugaban Accord Party na jihar, Victor Akande, ya ce masu kutse ɗin na da shirin lalata tsarin dijital na INEC tare da shigar da sakamakon zaɓen bogi cikin uwar garken hukumar. Ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta bincike tare da cafke waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.


Sai dai APC ta musanta zargin, inda kakakinta na jihar Osun, Kola Olabisi, ya bayyana shi a matsayin ƙarya marar tushe. Ya ce APC ba ta bukatar yin maguɗi domin ɗan takararta, Bola Oyebamiji, ya lashe zaɓen.


Olabisi ya kuma yi kira ga Accord Party da ta kai ƙarar lamarin ga ‘yan sanda idan tana da hujjar cewa akwai masu kutse da ake ɓoye a otal ɗin, yana mai cewa zargin na iya kasancewa sakamakon fargabar shan kaye a zaɓen.


#OsunElection #AccordParty #APC #INEC #Election2026 #Osun2026 #ElectionSecurity #CyberSecurity #BolaOyebamiji #AdemolaAdeleke

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill