ADC Ta Zargi Tinubu Da Cusa Mutanen Da Ake Zargi Da Cin Hanci A Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa
ADC Ta Zargi Tinubu Da Cusa Mutanen Da Ake Zargi Da Cin Hanci A Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa
Umar Nusaiba Ibrahim
Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, ta zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mayar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa na shekarar 2027 zuwa wani wuri da ake “gyara suna” na mutanen da ake fuskantar tambayoyi kan zargin cin hanci da rashawa.
Sakataren Yaɗa Labarai na ADC na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya nuna damuwa kan yadda aka saka tsohuwar Ministar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Betta Edu, da tsohuwar Shugabar NSITF, Ngozi Olejeme, cikin kwamitin. Jam’iyyar ta tambayi gwamnati ko an kammala bincike da shari’o’in da suka shafi waɗannan mutane, ko kuma nadin nasu wata hanya ce ta yin afuwa gare su.
ADC ta ce Betta Edu ta taɓa fuskantar dakatarwa daga Shugaba Tinubu bayan cece-kuce kan yunƙurin tura kuɗin Naira miliyan 585 zuwa wani asusun banki mai zaman kansa. Haka kuma, jam’iyyar ta tunatar da cewa Ngozi Olejeme ta taɓa fuskantar tuhuma daga EFCC kan zargin almundahana da kuɗaɗen gwamnati.
Jam’iyyar ta buƙaci gwamnati ta bayyana ko an wanke waɗannan mutane daga zarge-zargen da ake musu, tare da bayyana wanda ya wanke su da lokacin da aka yi hakan. ADC ta ce babban ƙalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta a zaɓen 2027 shi ne tsadar rayuwa da talauci, waɗanda ta ce ba za a iya kawar da su da kamfen kawai ba.
A gefe guda, ADC ta sake jaddada matsayinta na son a samar da wani tallafin man fetur da za a tsara shi da iyaka, kasafi na musamman da kuma sahihin binciken yadda ake kashe kuɗin, domin rage farashin fetur da kuma tsadar rayuwa. Jam’iyyar ta ce kafin gwamnati ta ce Najeriya ba za ta iya ɗaukar nauyin taimakon talakawa ba, ya kamata ta fara bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen gwamnati da kuma irin asarar da manufofinta suka jawo.
#ADC #Tinubu #2027Election #BettaEdu #NgoziOlejeme #Corruption #NigeriaPolitics #FuelSubsidy #CostOfLiving #NexviewTV

Comments
Post a Comment