An Cafke Wanda Ake Zargi Da Karɓar Kuɗin Fansa A Kwara


 

An Cafke Wanda Ake Zargi Da Karɓar Kuɗin Fansa A Kwara


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta cafke wani mutum da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane, a lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa a wani shagon POS.


An kama wanda ake zargin, Muhamodu Sanni, ne bayan jami’an tsaro sun zurfafa bincike kan sace wasu mutane uku a ƙauyen Obudu da ke Ƙaramar Hukumar Ilorin ta Gabas, sakamakon harin da aka kai yankin a ranar 28 ga Yuli.


Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce binciken ya mayar da hankali wajen gano hanyoyin da masu laifin ke amfani da su wajen sadarwa, safarar kuɗi da karɓar kuɗin fansa.


A cewar rundunar, bayan kama Sanni, ya bayar da wasu muhimman bayanai da suka haɗa da sunayen wasu daga cikin waɗanda ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar. Ana ci gaba da tantance bayanan domin ɗaukar matakan da suka dace.


Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kwara, Ojo Adekimi, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da farautar masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka. Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa.


#Kwara #YanSanda #GarkuwaDaMutane #KuɗinFansa #Tsaro #Nigeria #CrimeNews #Security #Ilorin

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill