An Kashe Mutane Fiye Da 20 A Sabon Hari A Plateau
An Kashe Mutane Fiye Da 20 A Sabon Hari A Plateau
Umar Nusaiba Ibrahim
Fiye da mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon hari da aka kai
a al’ummar Binper da ke gundumar Bwai, ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Plateau.
Rahotanni sun ce maharan sun mamaye yankin ne da tsakar dare, inda suka shiga gidaje tare da kai wa mutanen da ke barci hari. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan kashe wasu mutane uku a yankin, yayin da al’ummomin Fulani da Mwaghavul ke zargin juna da aikata kone-kone.
Shugaban Ƙungiyar Raya Mwaghavul ta Ƙasa, Bulus Dabit, ya tabbatar da harin. Wani ganau mai suna Daniel Musa ya ce maharan ɗauke da manyan makamai sun riƙa shiga gida-gida, suna buɗe ƙofofin gidajen mutane tare da kashe su a cikin barcinsu.
Ya ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar sama da mutane 20, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka, sannan wasu kuma har yanzu ba a san inda suke ba. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba.
#Plateau #Mangu #BreakingNews #NigeriaNews #Security #Attack #Insecurity #NexviewTV #NewsUpdate #Nigeria #Breaking #LatestNews

Comments
Post a Comment