An Tura Wani Gidan Gyaran Hali Kan Zargin Satar Takalma A Kano
An Tura Wani Gidan Gyaran Hali Kan Zargin Satar Takalma A Kano
Umar Nusaiba Ibrahim
Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai suna Muhammad Najib Rimin Kebe, bisa zargin satar takalma a wani masallaci da ke cikin harabar Kotunan Norman’s Land a Kano.
An gurfanar da Najib a gaban kotun ne bayan an zarge shi da yawan zuwa masallacin domin satar takalman masu ibada. Rahoton ya ce daga cikin wadanda aka ce an sace wa takalman akwai ma’aikatan kotu da jami’an tsaro.
Bayan sauraron bayanan da aka gabatar mata, kotun ta bayar da umarnin a tura wanda ake zargin gidan gyaran hali, yayin da ake ci gaba da shari’ar.
An dage ci gaba da sauraron karar zuwa 28 ga Agusta 2026, lokacin da kotun za ta ci gaba da duba batun.
#Kano #DailyTrust #SatarTakalma #KotunKano #GidanGyaranHali #KanoNews #Labarai #NigeriaNews #Tsaro #CrimeNews #NormanLand #Nijeriya

Comments
Post a Comment