ASUU Ta Bai Wa Jami’o’i 20 Izinin Fara Shirye-shiryen Yajin Aiki


 


ASUU Ta Bai Wa Jami’o’i 20 Izinin Fara Shirye-shiryen Yajin Aiki


Daga Umar Nusaiba ibrahim


Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bai wa rassa 20 na jami’o’i izinin fara shirye-shiryen yajin aiki, bisa zargin jinkirin aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da Gwamnatin Tarayya a shekarar 2025.


ASUU ta ce jami’o’in da abin ya shafa za su bai wa hukumominsu wa’adin kwanaki 14 domin magance matsalolin da suke gabatarwa, kafin fara yajin aiki idan ba a biya buƙatunsu ba. Matakin ya biyo bayan taron NEC na ƙungiyar da aka gudanar a Jami’ar Abuja a ranakun 8 da 9 ga Agusta 2026.


Daga cikin jami’o’in akwai Jami’ar Jihar Nasarawa, IBB University Lapai, Gombe State University, Plateau State University, Abia State University, Imo State University, Kaduna State University, Aliko Dangote University of Science and Technology da Northwest University Kano.


A halin yanzu, rassa na ASUU a Jami’ar Jihar Nasarawa da Jami’ar Jihar Imo sun riga sun fara yajin aiki na sai baba-ta-gani. A Nasarawa, malaman sun ce ana bin su hakkoki da suka haura Naira biliyan uku, yayin da a Imo kuma aka yi zargin rashin aiwatar da yarjejeniyar 2025 da kuma wasu basussukan albashi da alawus-alawus.


ASUU ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa, amma ba za ta dakatar da yajin aikin ba har sai an magance buƙatunta. Ƙungiyar ta kuma shirya gudanar da wani taron gaggawa a ƙarshen Agusta ko farkon Satumba domin duba halin da ake ciki da ɗaukar matakin gaba.


#ASUU #YajinAiki #JamiOI #Ilimi #Nigeria #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill