ASUU Ta Koka Kan Ƙarancin Albashin Malaman Jami’o’in Jihar Legas
ASUU Ta Koka Kan Ƙarancin Albashin Malaman Jami’o’in Jihar Legas
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi zargin cewa manyan farfesoshi a jami’o’in gwamnatin Jihar Legas na karɓar albashi ƙasa da shugabannin makarantun sakandare na gwamnati a jihar.
A wani taron manema labarai da rassan ASUU na Jami’ar Jihar Legas (LASU), LASUSTECH da LASUED suka gudanar, Kodinetan shiyyar ASUU, Kwamared Oluwaseun Babalola, ya ce gwamnatin jihar ta kasa aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya da ASUU suka cimma a shekarar 2025, duk da cewa an tsara fara aiwatar da ita daga ranar 1 ga Janairun 2026.
Babalola ya bayyana cewa wannan jinkiri ya jefa malaman jami’o’i cikin matsin tattalin arziki, tare da ƙara musu harajin albashi duk da cewa ba a fara biyan sabon tsarin albashin ba. Ya kuma yi ikirarin cewa shugaban makarantar sakandare na gwamnati na karɓar kusan N799,000 a wata, yayin da babu wani farfesa a LASU da ke samun irin wannan albashi.
ASUU ta kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da ya gaggauta aiwatar da yarjejeniyar, ya magance matsalolin jin daɗin ma’aikata, tare da mayar da shugabannin ASUU biyar da aka kora daga aiki, waɗanda ƙungiyar ta ce an hukunta su ne saboda ayyukan ƙungiya.
Haka kuma, shugabannin ASUU na LASUED da LASUSTECH sun yi zargin cewa rashin sauraron koke-koken malamai, barazana ga masu ayyukan ƙungiya da kuma jinkirin karin girma na ci gaba da rage ƙwarin gwiwar malaman jami’o’in.
#ASUU #LASU #LASUSTECH #LASUED #Ilimi #Albashi #Legas #Najeriya #NexviewTV

Comments
Post a Comment