Ba Rashin Kyakkyawan Yanayin Aiki Ne Ya Sa Malamai Ke Barin KASU Ba – VC
Ba Rashin Kyakkyawan Yanayin Aiki Ne Ya Sa Malamai Ke Barin KASU Ba – VC
Umar Nusaiba Ibrahim
Shugabancin Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ya musanta ikirarin kungiyar ASUU reshen jami’ar cewa sama da malaman jami’a 200, ciki har da farfesoshi, sun bar jami’ar saboda rashin kyakkyawan yanayin aiki. Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya ce sauyin wurin aiki tsakanin jami’o’i abu ne da ya zama ruwan dare a duniya, don haka bai kamata a fassara shi a matsayin matsalar yanayin aiki a KASU ba.
Musa ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, bayan da ASUU-KASU ta bai wa gwamnatin Jihar Kaduna wa’adin makonni biyu kan aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya da ASUU suka cimma a 2025, da kuma wasu bukatun jin dadin ma’aikata. ASUU ta ce asarar kwararrun malamai sama da 200 na iya jefa jami’ar cikin matsala wajen maye gurbin gogaggun malamai da iliminsu.
Sai dai KASU ta ce jami’ar na ci gaba da rike wasu fitattun masana da ke cikin kashi biyu cikin 100 na manyan masana kimiyya a duniya. Ta kuma bayyana cewa jami’ar ta samu sama da fam miliyan 945 na kudaden bincike cikin shekaru uku, yayin da gwamnatin jihar ta zuba sama da Naira miliyan 290 wajen tantance albarkatu da kuma tabbatar da ingancin shirye-shiryen karatu sama da 90.
Dangane da jin dadin ma’aikata, Mataimakin Shugaban Jami’ar ya ce gwamnatin jihar ta biya bashin albashin da aka gada tun daga watan Mayun 2022, tare da ci gaba da biyan albashi kowane wata. Ya kuma ce an kashe sama da Naira biliyan daya wajen tallafin karatu tare da rage kudin makaranta da kashi 50 cikin 100. Ya bukaci ASUU-KASU ta sake duba matsayinta tare da komawa teburin tattaunawa domin warware matsalolin da ke tsakaninsu.
#KASU #ASUU #KadunaStateUniversity #EducationNigeria #JamiarKaduna #Malamai #NigeriaEducation #ASUUKASU #Kaduna #NexviewTV

Comments
Post a Comment