Davido ya yi barazanar kai ƙorafi ga Trump idan aka yi maguɗi a zaɓen Osun
Davido ya yi barazanar kai ƙorafi ga Trump idan aka yi maguɗi a zaɓen Osun
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya nuna damuwarsa kan yadda za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun da ke tafe, inda ya yi gargaɗin cewa ba zai kyale duk wani yunƙurin maguɗi ko rashin adalci ba.
Davido ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa kai tsaye da ya yi a kafafen sada zumunta. Ya ce idan aka samu wata matsala ko maguɗi a lokacin zaɓen, zai ɗauki mataki tare da kai ƙorafi har zuwa wajen Shugaban Amurka, Donald Trump.
Mawakin ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da jami’an tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa, da su tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, gaskiya da adalci.
Ya kuma jaddada cewa wajibi ne a mutunta ƙuri’un jama’a tare da tabbatar da cewa sakamakon zaɓen ya kasance abin da masu kaɗa ƙuri’a suka zaɓa, ba tare da tsangwama ko maguɗi ba.
#Davido #OsunElection #Osun #Trump #INEC #ZabenOsun #Najeriya #NexviewTV #LabaranYau

Comments
Post a Comment