EFCC Ta Umarci First Bank Ya Dakatar Da Hada-hadar Asusun Gwamnatin Osun


 


EFCC Ta Umarci First Bank Ya Dakatar Da Hada-hadar Asusun Gwamnatin Osun


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC) ta umarci First Bank ya sanya takunkumi kan asusun Gwamnatin Jihar Osun. Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne ba tare da samun umarnin kotu ba.


A cewarsa, matakin yana da alaƙa da siyasa, kuma an ƙirƙiro shi ne domin kawo cikas ga gwamnatinsa gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2026.


Sai dai EFCC ta ce ta bayar da umarnin ne bisa tanade-tanaden Dokar Kafa EFCC ta shekarar 2004 da kuma Dokar Hana Wanke Kuɗaɗen Haramtacciyar Hanya ta shekarar 2022.


A halin da ake ciki, Gwamnatin Jihar Osun ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Osogbo domin ƙalubalantar matakin, tare da neman kotu ta soke umarnin da aka bai wa bankin.


#EFCC #FirstBank #Osun #AdemolaAdeleke #Siyasa #Najeriya #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill