Fargaba Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Dattijo Mai Shekara 90 A Neja


 

Fargaba Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Dattijo Mai Shekara 90 A Neja


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dattijo mai shekaru 90, Malam Abubakar Lafiya, a yankin Ka’ada da ke gundumar Dekara, Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.


Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, lokacin da ’yan bindigar suka kai farmaki gidan dattijon, wanda shi ne mai unguwar ƙauyen. An ce sun yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su yi awon gaba da shi.


Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa dattijon da aka sace shi ne mahaifin Hakimin Dekara na yanzu.


Ya ce sace dattijon ya jefa al’ummar Ka’ada, Dekara da sauran ƙauyukan da ke makwabtaka da su cikin fargaba, musamman ganin cewa shekarunsa sun kai 90.


Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin takaici da tashin hankali, tare da ci gaba da addu’ar Allah Ya dawo da dattijon lafiya.


Sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto shi tare da tabbatar da tsaron lafiyarsa.


Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja bai yi nasara ba, domin ba a samu damar tuntuɓar mai magana da yawun rundunar ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.



#Neja #Borgu #Garkuwa #YanBindiga #Tsaro #Nigeria #BreakingNews #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill