FG Na Shirin Amfani Da Ribar Hannun Jari Da Ba A Karɓa Ba Wajen Tallafa Wa NELFUND
FG Na Shirin Amfani Da Ribar Hannun Jari Da Ba A Karɓa Ba Wajen Tallafa Wa NELFUND
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin amfani da wasu kuɗaɗen dividend da ba a karɓa ba, da kuma kuɗaɗen da ke cikin asusun dormant, wajen ƙarfafa Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma bayar da umarnin karkatar da kuɗaɗen da EFCC ta kwato, waɗanda babu wata shari’a ko wani cikas na doka a kansu, zuwa NELFUND domin tallafa wa shirin lamunin ɗalibai.
Ministan Ilimi, Dr Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, inda ya ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da cewa NELFUND na da isasshen kuɗi kuma zai iya ci gaba da gudanar da ayyukansa yayin da yawan masu cin gajiyar shirin ke ƙaruwa.
Alausa ya ce Attorney-General na Tarayya zai haɗa kai da Ministocin Ilimi da Kuɗi da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da cewa tsarin ya dace da doka. Ya kuma ce za a iya yin gyare-gyare ga dokokin da suka kafa asusun idan hakan ya zama dole.
A halin yanzu, sama da ɗalibai miliyan 1.2 ne ke cin gajiyar NELFUND, yayin da aka raba sama da Naira biliyan 322 domin biyan kuɗaɗen makarantu da alawus-alawus na ɗalibai zuwa ranar 8 ga Agusta.
#NELFUND #Tinubu #Education #StudentLoan #Nigeria #FG #NexviewTV

Comments
Post a Comment