Gwamnan Kebbi Ya Miƙa Yara 5 Da Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Mutane Ga Iyayensu
Gwamnan Kebbi Ya Miƙa Yara 5 Da Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Mutane Ga Iyayensu
Daga: Ibrahim Sani Isyaku
Gwamnan Kebbi Ya Miƙa Yara 5 Da Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Mutane Ga Iyayensu.
Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya miƙa yara biyar da aka ceto daga hannun masu safarar mutane ga iyayensu a Birnin Kebbi.
Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane (NAPTIP) ce ta miƙa yaran ga gwamnatin jihar kafin a mayar da su ga iyayensu.
Gwamnan, wanda mataimakinsa, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya wakilta, ya buƙaci iyaye su ƙara kula da ‘ya’yansu, yana mai cewa yara ni’ima ce daga Allah.
Ya gargaɗi duk wanda aka kama da hannu wajen safarar yaran cewa zai fuskanci hukunci a gaban doka.
Mataimakin gwamnan ya kuma yaba wa NAPTIP kan kokarinta, tare da alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba hukumar goyon baya.
Kwamandan NAPTIP na Kebbi, Misbahu Iya Kaura, ya ce sun gano wata ƙungiyar da ke safarar yara tsakanin Kebbi, Zamfara, Neja da Edo.
Ya ce an kama mutane biyar a Ribah, Gusau da Kontagora, yayin da aka ceto yaran, maza uku da mata biyu, a Jihar Zamfara lokacin da ake ƙoƙarin kai su Edo.
A cewar Kaura, masu safarar suna yaudarar iyaye da cewa za su kai ‘ya’yansu makaranta kyauta a wasu jihohi.
Daga nan suke fitar da yaran daga gida zuwa wurare masu nisa.
Ya ce bincike ya nuna cewa an dade ana safarar yara daga Masarautar Zuru zuwa Kudancin Nijeriya, har ma wasu aka kai su Ghana.
Kwamandan ya yi kira ga iyaye, sarakuna da malamai da su kara wayar da kan jama’a kan illar bai wa baki yara bisa alkawarin kai su makaranta.
#FaithAndPolitics #OneNigeria #Nigeria2027
#NEXVIEWTV #NEXVIEWNews #NEXVIEW

Comments
Post a Comment