Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Haɗin Kan Jama’a Wajen Inganta Tsaro


 

Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Haɗin Kan Jama’a Wajen Inganta Tsaro


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Gwamnatin Tarayya ta yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, hukumomin gwamnati, al’umma da kafafen yaɗa labarai domin magance matsalolin tsaro a Najeriya.


Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce amfani da ƙarfin soji kaɗai ba zai magance matsalar tsaro ba, yana mai cewa haɗin kan jama’a da hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci.


Ya kuma yi gargadin cewa labaran ƙarya da yaɗa jita-jita na iya zama barazana ga tsaron ƙasa, inda ya buƙaci a riƙa bai wa jama’a sahihan bayanai cikin gaggawa.


Shi ma Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Cikin Gida, Manjo-Janar Adeyinka Famadewa, ya ce bayanai na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron ƙasa, musamman wajen dakile barazanar tsaro da yaɗa bayanan ƙarya.


Gwamnatin ta tabbatar da cewa za ta ƙara haɗin gwiwa da hukumomin tsaro da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasar.


#TsaronKasa #GwamnatinTarayya #HadinGwiwa #Tsaro #Nigeria #CitizenSecurity #NationalSecurity #MohammedIdris

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill