Hare-haren Intanet Ne Babbar Barazana Ga Zaben 2027 – Janar Musa
Hare-haren Intanet Ne Babbar Barazana Ga Zaben 2027 – Janar Musa
Umar Nusaiba Ibrahim
Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya ce hare-haren intanet na daga cikin manyan barazanar tsaron zaben 2027. Ya bayyana hakan ne yayin lacca ta jaridar Blueprint kan tsaro da sahihancin zaben 2027, inda ya ce barazanar tsaro ta sauya daga fagen zahiri zuwa sararin intanet.
Musa, wanda Babban Janar Olufemi Akinjobi ya wakilta, ya ce fasahar zamani da basirar wucin gadi na iya taimakawa ci gaban kasa, amma kuma suna haifar da sabbin barazanar tsaro. Ya ce masu aikata laifi na iya amfani da kwamfuta wajen yada labaran karya, sarrafa hotuna, bidiyoyi da muryoyi domin yaudarar jama’a da rage amincewarsu da tsarin dimokuradiyya.
Ministan ya jaddada cewa tsaron zabe bai kamata ya tsaya kan kare rumfunan zabe kawai ba, sai an hada da kare tsarin intanet, dakile yada bayanan karya da kuma tabbatar da sahihancin bayanai. Ya ce shirye-shiryen zaben 2027 ya kamata su zama wani shiri na kasa baki daya domin karfafa dimokuradiyya da tabbatar da cewa ‘yan Najeriya za su kada kuri’a cikin aminci da ‘yanci.
A nasa bangaren, Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bukaci a fara shirye-shiryen tsaron zaben tun kafin lokacin yakin neman zabe. Ya ce ya kamata a mai da hankali kan matsalolin ‘yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane, rikicin al’umma, yada labaran karya, kutsen intanet, sayen kuri’u da kuma daukar matasa cikin rikicin siyasa.
#Zaben2027 #TsaronZabe #CyberAttack #HareHarenIntanet #Nigeria2027 #ElectionSecurity #JanarMusa #INEC #Dimokuradiyya #NigeriaNews #NexviewTV

Comments
Post a Comment