Idan kuka fara aiki ku karasa" inji ministan ilimi
"Idan kuka fara aiki ku karasa" inji ministan ilimi
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya gargadi jami’an da ke kula da shirin Nigeria Education Sector Renewal Initiative (NESRI) da su daina ɗaukar fara aiki a matsayin kammala shi. Ya ce daga yanzu, gwamnati za ta fi mayar da hankali wajen tabbatar da cewa duk wani aiki da aka fara an kammala shi yadda ya kamata.
Alausa ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin taron nazarin ayyukan NESRI na tsawon watanni shida. Ya ce manufar taron ba bikin nasarorin da aka samu ba ce, sai dai tantance abubuwan da aka kammala, waɗanda suka rage da kuma hanyoyin da za a bi wajen kammala ayyukan da ake yi.
Ministan ya ce jami’an da ke kula da shirye-shiryen za su kasance da cikakken alhakin ayyukan da aka damƙa musu, tare da gano matsalolin da ke kawo tsaiko da kuma tsara wa’adin da za a kammala su. Ya kuma jaddada cewa nasarar Ma’aikatar Ilimi ba za ta dogara da yawan shirye-shiryen da aka ƙaddamar ko tarurrukan da aka gudanar ba, sai dai sakamakon da jama’a ke gani a makarantu da tsarin ilimi baki ɗaya.
Alausa ya ce shirin NESRI ya shafi muhimman fannoni da suka haɗa da ilimin sana’o’i da fasaha, STEM, yaƙi da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, ilimin ’ya’ya mata, inganta ingancin ilimi, bayanan ilimi da kuma amfani da fasahar zamani. Ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ma’aikatar za ta ci gaba da aiwatar da ajandar ilimi ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar samun ingantaccen ilimi da ƙwarewar da za ta taimaka masa a rayuwa.
#Alausa #Ilimi #NESRI #NigeriaEducation #EducationReform #FederalGovernment #EducationSector #Tinubu #KaratunYara #IngantaccenIlimi #NigeriaNews #NexviewTV

Comments
Post a Comment