JAMB Ta Gargadi ’Yan UTME Da DE Kan Kurakuran Ƙirƙirar Profile
JAMB Ta Gargadi ’Yan UTME Da DE Kan Kurakuran Ƙirƙirar Profile
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Najeriya (JAMB) ta gargadi masu shirin rubuta jarabawar UTME da Direct Entry (DE) da su guji yin kuskure yayin ƙirƙirar bayanan profile ɗinsu.
JAMB ta ce ƙaramin kuskure wajen shigar da bayanai na iya haifar da babbar matsala daga baya a yayin tsarin karɓar ɗalibai zuwa manyan makarantun ƙasa.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wani sabon faifan bidiyo da ta wallafa a ƙarƙashin shirinta na “JAMB Explained” a shafinta na X ranar Laraba.
JAMB ta jaddada cewa masu neman shiga jami’a su tabbatar da cewa sunansu, ranar haihuwa da sauran bayanan da ke da alaƙa da NIN ɗinsu sun yi daidai kafin su ƙirƙiri profile.
Hukumar ta ce bayanan ’yan takara ana samo su ne daga bayanan da ke hannun Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC), ba daga JAMB ba.
Saboda haka, JAMB ta ce idan akwai kuskure a suna ko ranar haihuwa, ba za ta iya gyara bayanan bayan an kammala rajista ba.
Hukumar ta kuma gargadi ’yan takara kada su ɗauka cewa samun affidavit kaɗai zai sa a gyara bayanan da ke cikin tsarin JAMB.
JAMB ta bukaci masu shirin UTME da DE da su tabbatar da sahihancin bayanansu tun kafin fara ƙirƙirar profile, domin kauce wa matsaloli a lokacin rajista da karɓar gurbin karatu.
#JAMB #UTME #DirectEntry #DE #NIN #JAMBRegistration #NigeriaEducation #EducationNews

Comments
Post a Comment