Jami’ar Tarayya Dutse Ta Samu Naira Miliyan 53 Don Binciken ‘Yan Bindiga Da Sauro
Jami’ar Tarayya Dutse Ta Samu Naira Miliyan 53 Don Binciken ‘Yan Bindiga Da Sauro
Umar Nusaiba Ibrahim
Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa, ta samu tallafin bincike guda biyu na Naira miliyan 53 daga Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund), domin gudanar da bincike kan matsalar ‘yan bindiga a Arewa da kuma hanyoyin dakile yaduwar sauro a Najeriya.
Jami’ar ta ce Naira miliyan 25 za a bai wa binciken da Farfesa Ado Jangargari zai jagoranta, mai taken amfani da fasaha wajen samar wa makiyaya hanyoyin samun kudin shiga ba tare da dogaro da noma ba, domin rage matsalar ‘yan bindiga da garkuwa da mutane. Sauran Naira miliyan 28 za a yi amfani da su wajen binciken da Farfesa Joshua Balogun zai jagoranta kan samar da na’urar dakile sauro a cikin gidaje.
A cewar jami’ar, za a gudanar da dukkan ayyukan binciken cikin watanni 24, inda ake sa ran za su samar da hanyoyin magance wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar al’umma. Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ahmad Gumel, ya taya malaman murna tare da bukatar su tabbatar da an gudanar da binciken cikin lokaci kuma cikin inganci.
Jami’ar ta kuma bayyana cewa za ta sanya ido sosai kan ayyukan binciken domin tabbatar da sun cika ka’idojin TETFund tare da samar da sakamakon da zai amfani al’ummar Jigawa da Najeriya baki daya. Jami’ar ta ce tana ci gaba da karfafa wa malamanta gwiwar neman karin tallafin bincike daga TETFund da sauran kungiyoyin duniya.
#FUDutse #Jigawa #TETFund #Bincike #ResearchGrant #YakiDaYanBindiga #DakileSauro #Tsaro #Lafiya #EducationNigeria #NigerianUniversities #NexviewTV

Comments
Post a Comment