Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Da Za Ta Kayyade Ƙarin Kuɗin Makarantu Masu Zaman Kansu.

 


Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Da Za Ta Kayyade Ƙarin Kuɗin Makarantu Masu Zaman Kansu.


Daga Umar Nusaiba Ibrahim


Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudirin gyaran dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta shekarar 2026, domin daidaita yadda makarantu masu zaman kansu ke gudanar da harkokinsu da kuma kare iyaye daga yawan ƙarin kuɗin makaranta.


Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wata makaranta mai zaman kanta ta firamare ko sakandare dole ne ta tuntubi ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) kafin ta ƙara kuɗin makaranta. Haka kuma, duk wani ƙarin kuɗi da za a yi ba zai wuce kashi 10 cikin ɗari na kuɗin da ake biya a halin yanzu ba.


Dokar ta kuma haramta wa makarantu karɓar kuɗin rijistar jarabawa sama da kashi 10 cikin ɗari na abin da hukumomin shirya jarabawa irin su WAEC, NECO da NBTE suka kayyade. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage wa iyaye nauyin kuɗaɗe tare da tabbatar da gaskiya wajen tafiyar da harkokin ilimi.


Bugu da ƙari, an rage kuɗin da makarantu masu zaman kansu ke biya Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu daga kashi 15 cikin ɗari zuwa kashi biyar cikin ɗari, domin sauƙaƙa wa masu makarantu gudanar da ayyukansu.


Dokar ta kuma tanadi cewa mukamin Babban Sakataren Hukumar zai kasance na gogaggen malami ko ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya wanda ya kai aƙalla mataki na 14 (Grade Level 14), domin tabbatar da ingantaccen jagoranci da gudanarwa.


Jagoran Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini, ya bayyana cewa waɗannan gyare-gyaren za su taimaka wajen inganta tsarin ilimi, ƙarfafa sa ido kan makarantu masu zaman kansu, da kuma kare haƙƙin iyaye da ɗalibai a faɗin Jihar Kano.


Dokar dai na jiran sahalewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kafin ta fara aiki a hukumance.


Hashtags:

#Kano #MajalisarKano #Ilimi #PrivateSchools #PTA #WAEC #NECO #NBTE #EducationNews #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill