Mutum Biyar Da Ake Zargin ’Yan ISWAP Ne Sun Mutu Sakamakon Fashewar Bam A Borno
Mutum Biyar Da Ake Zargin ’Yan ISWAP Ne Sun Mutu Sakamakon Fashewar Bam A Borno
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Mutum biyar da ake zargin mambobin ƙungiyar ISWAP ne sun mutu bayan wani bam ya fashe a lokacin da suke haɗa na’urorin fashewa (IED) a ƙauyen Maina Daya da ke ƙaramar hukumar Marte a Jihar Borno.
Rahotanni sun ce waɗanda suka mutu sun haɗa da wani jami’in lafiya na ƙungiyar, ƙwararrun masu haɗa bama-bamai guda biyu daga ƙasashen Larabawa, da kuma wasu ƙwararrun masu kera bama-bamai na ISWAP guda biyu.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa fashewar ta faru ne yayin da ake shirya bama-baman da ake zargin za a kai hare-hare da su a kan hanyoyin sojoji.
Masana harkokin tsaro sun ce wannan lamari na iya rage ƙarfin ISWAP na kai hare-haren bama-bamai na ɗan wani lokaci, yayin da rundunar Operation HADIN KAI ta ƙara tsaurara sintiri da hare-haren da take kai wa a yankunan Monguno, Marte da Gamboru Ngala domin hana ƙungiyar sake farfaɗowa.
#Borno
#ISWAP
#OperationHadinKai
#Tsaro
#YakiDaTaaddanci
#NigerianArmy
#Marte
#Monguno
#BreakingNews
#NexviewTV

Comments
Post a Comment