NERDC Ta Musanta Takardar Neman Tallafin Buga Sabon Manhajar Karatu





NERDC Ta Musanta Takardar Neman Tallafin Buga Sabon Manhajar Karatu

Daga Umar Nusaiba Ibrahim 

Hukumar Bincike da Raya Manhajar Ilimi ta Najeriya (NERDC) ta musanta wata takarda da ke yawo a kafafen sadarwa wadda ke neman tallafin kuɗi domin bugawa da rarraba sabuwar manhajar ilimin bai ɗaya ta shekarar karatu ta 2026/2027.

Sakataren Zartarwar hukumar, Farfesa Salisu Shehu, ya bayyana takardar a matsayin ta bogi, marar tushe kuma ba ta fito daga hukumar ba. Ya buƙaci hukumomin gwamnati, cibiyoyin ilimi, abokan hulɗa da sauran jama’a da su yi watsi da ita.

A cikin sanarwar da ya sanya wa hannu a Abuja, Shehu ya ce NERDC ba ta fitar da wata takarda ko wasiƙa da ke neman tallafin kuɗi daga kowace hukuma ko ƙungiya domin bugawa ko rarraba sabuwar manhajar karatun.

Ya ƙara da cewa hukumar ta riga ta tanadi hanyoyin bugawa da rarraba manhajar ta hannun hukumomin ilimi na tarayya da jihohi, don haka babu wani mutum ko ƙungiya da aka ba izinin neman tallafi a madadin NERDC.

Hukumar ta kuma jaddada cewa duk wani sahihin bayani game da sabuwar manhajar ilimi za a riƙa fitar da shi ne kawai ta hanyoyin sadarwa na hukuma na NERDC.

Sabuwar manhajar ilimin bai ɗaya za a fara aiwatar da ita ne a shekarar karatu ta 2026/2027, inda aka sabunta ta domin ƙara ƙarfafa ilimin karatu da lissafi, fasahar zamani, kasuwanci, tarbiyyar ƙasa da kuma ƙwarewar da ake buƙata a ƙarni na 21.


#NERDC #Education #Curriculum #Nigeria #BasicEducation #NexviewTV



Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill