Oloyede: Iyaye Ne Ke Haddasa Magudin Jarabawa, Ba Ɗalibai Ba


 

Oloyede: Iyaye Ne Ke Haddasa Magudin Jarabawa, Ba Ɗalibai Ba


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Tsohon Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce iyaye ne ke taka muhimmiyar rawa wajen haddasa magudin jarabawa a Najeriya, ba ɗalibai ba. Ya bayyana cewa a tsawon shekaru 10 da ya yi yana jagorantar JAMB, abin da ya fi ba shi ciwo shi ne yadda wasu iyaye ke shirya wa ‘ya’yansu hanyoyin yin magudi domin samun gurbin karatu.


Oloyede ya ce mafi yawan ɗalibai ba su ne ke ƙirƙirar wannan laifi ba, sai dai iyayensu ne ke tura su zuwa halayen rashin gaskiya. Ya kuma jaddada cewa babu wata jami’a da ke da ikon ba da gurbin karatun digiri ba tare da bin tsarin JAMB ba, domin yin hakan ya saɓa wa doka.


Ya kuma yi bayani kan batun da aka yi ta kira “maciji ya haɗiye kuɗi”, inda ya ce lamarin ya faru ne kafin ya zama shugaban JAMB, kuma babu wani maciji da ya haɗiye kuɗi, sai dai an yi ta yaɗa labarin ta hanyar da ta jawo ce-ce-ku-ce. Oloyede ya kammala wa’adinsa na shugabancin JAMB a ranar 31 ga Yuli, 2026.


#NexviewTV

#JAMB

#IshaqOloyede

#ExamMalpractice

#EducationNews

#NigeriaEducation

#UTME

#Parents

#Admission

#BreakingNews

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill