Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Alkawarin Samun Mafita Cikin Shekara Ɗaya


 

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Alkawarin Samun Mafita Cikin Shekara Ɗaya


Umar Nusaiba Ibrahim 


Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya cikin shekara guda idan aka zaɓe shi a zaben 2027.


Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya ce gwamnatinsa za ta ƙara yawan jami’an tsaro tare da samar musu da kayan aiki da isasshen kuɗin gudanar da ayyukansu.


Ya kuma ce za a tallafa wa matasa da jari domin su kafa sana’o’i, yana mai cewa rashin aikin yi na daga cikin abubuwan da ke sanya wasu matasa shiga aikata laifuka.


Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi alkawarin ƙarfafa haɗin gwiwar sojojin ƙasashen ECOWAS, tare da ƙoƙarin dawo da ECOMOG domin taimakawa wajen magance matsalar tsaro a yankin.


Game da zaben 2027, Atiku ya nuna shakku kan INEC, amma ya bukaci ’yan Najeriya su fito ƙuri’a, su kare ƙuri’unsu kuma su tabbatar an ƙidaya su yadda ya kamata.


#AtikuAbubakar #2027Election #RashinTsaro #Tsaro #Nigeria #ADC #ECOWAS #INEC #SiyasarNajeriya #NigerianPolitics

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill