Read To Live Ta Yi Allah-Wadai Da Shirin Ƙara Kuɗin WAEC Da NECO Ba Tare Da Bayyananniyar Hujja Ba
Read To Live Ta Yi Allah-Wadai Da Shirin Ƙara Kuɗin WAEC Da NECO Ba Tare Da Bayyananniyar Hujja Ba
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Ƙungiyar masu bincike kan manufofin ilimi ta Read To Live Initiative ta buƙaci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta bayyana cikakken bayanin kuɗaɗen da suka sa aka ba da shawarar ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000 kafin a yanke hukunci na ƙarshe. Ƙungiyar ta ce dakatar da shirin ƙarin kuɗin kaɗai bai wadatar ba, tana mai jaddada cewa duk wata tattaunawa da za a yi da masu ruwa da tsaki dole ne ta kasance bisa hujjoji da bayanai da aka bayyana wa jama’a.
Daraktan ƙungiyar, Jacob Sule, ya ce idan da gaske an yi nazarin kuɗaɗen gudanar da jarabawar kafin gabatar da wannan shawara, ya kamata a wallafa wannan nazari tun lokacin da aka sanar da shirin. Ya ƙara da cewa ƙara kuɗin jarabawar da zai shafi miliyoyin ɗalibai ba ƙaramin sauyi ba ne, don haka ya dace gwamnati ta bayyana hujjojin da suka sa aka ɗauki wannan mataki.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci Ma’aikatar Ilimi, WAEC, NECO, Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnati su fitar da cikakken bayanin nazarin kuɗaɗe da rahotannin binciken kuɗaɗen hukumomin jarabawar, tare da tantance yadda ƙarin kuɗin zai shafi iyalai masu ƙaramin ƙarfi kafin a sanar da sabon kuɗin rajistar jarabawar.
#WAEC #NECO #Education #Nigeria #ExamFees #FederalMinistryOfEducation #ReadToLiveInitiative #NexviewNews

Comments
Post a Comment