Tinubu: Hausawa ginshiƙai ne na ci gaban Najeriya.


 

Tinubu: Hausawa ginshiƙai ne na ci gaban Najeriya.

Daga: Ibrahim Sani Isyaku 


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana al’ummar Hausawa a matsayin manyan ginshiƙai da ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya da ci gabanta.


Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙon 2da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, domin taya al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, wadda ake gudanar da bikin ta a fadar Mai Martaba Sarkin Daura da ke Katsina. 


Shugaban ya kuma yaba da yadda harshen Hausa ya bunƙasa, yana mai cewa ya zama ɗaya daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su wajen haɗin kan al’umma da harkokin kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.


Tinubu ya taya ɗaukacin al’ummar Hausawa murnar wannan rana, tare da bayyana muhimmancin al’adun Hausa da harshen wajen haɗa kan jama’a.


Ranar Hausa, wadda kuma ake kira Ranar Hausa ta Duniya, ana bikin ta a ranar 26 ga Agusta na kowace shekara. An fara ƙaddamar da ita ne a matsayin wani yunƙuri na ƙarfafa amfani da harshen Hausa a kafafen sada zumunta da kuma wayar da kan jama’a game da muhimmancin al’adun Hausa. 


Bikin ya ƙara samun karɓuwa a sassa daban-daban na duniya, ciki har da ƙasashen Afirka da wasu sassan Turai, Gabas ta Tsakiya, Asiya da Amurka, duk da cewa har yanzu ba ta samu amincewar Majalisar Ɗinkin Duniya a hukumance ba. 


A sakonsa, Tinubu ya jaddada cewa gudunmawar Hausawa na da muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya da ci gabanta, yayin da harshen Hausa ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan harsunan da ake magana da su a Najeriya da Afirka.


#FaithAndPolitics #OneNigeria #Nigeria2027

#NEXVIEWTV #NEXVIEWNews #NEXVIEW

#DAILY TRUST

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill