Tinubu Na Taimakon Talakawa, Inji Gwamnan Sokoto
Tinubu Na Taimakon Talakawa, Inji Gwamnan Sokoto
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce ikirarin da ‘yan adawa ke yi na cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai kawo wani sauyi a rayuwar ‘yan Najeriya cikin shekaru uku ba, ba komai ba ne face farfaganda. Gwamnan ya ce tasirin manufofin gwamnatin Tinubu a rayuwar al’umma a bayyane yake.
Ahmed Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin taron kasa na yini guda kan “Inganta Shigar Jama’a Cikin Siyasa da Adalcin Zamantakewa a Matsayin Mafita Ga Hadin Kan Kasa da Ci Gaba”, wanda kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya a Jos, Jihar Plateau.
Gwamnan ya ce gwamnatin tarayya na samar da tallafin abinci da taki kyauta, tare da daukar wasu matakai domin rage radadin talakawa. Ya ce dukkanin abubuwan da gwamnatin Tinubu ta yi an rubuta su tare da adana bayanansu, yana mai cewa duk wanda bai ga tasirin shugaban kasar ba, kamar bai zauna a Najeriya ba.
Gwamnan Sokoto ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su sake zabar Shugaba Tinubu a zaben 2027, yana mai cewa yana da yakinin shugaban kasar ba zai kunyata Najeriya ba. Taron ya samu halartar Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.
Sai dai ‘yan adawa sun yi watsi da wannan matsaya. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki bayanin Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, kan nasarorin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa wahalhalun tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta ba za a iya boye su da bayanan gwamnati ba. Wannan ya nuna bambancin ra’ayi tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan adawa kan tasirin manufofin tattalin arzikin Tinubu.
#Tinubu #AhmedAliyu #Sokoto #JIBWIS #Nigeria #Tinubu2027 #AtikuAbubakar #ADC #NigerianPolitics #NexviewTV

Comments
Post a Comment