Tinubu Ya Bukaci ’Yan Najeriya Mazauna Ƙetare Su Zuba Jari A Gida
Tinubu Ya Bukaci ’Yan Najeriya Mazauna Ƙetare Su Zuba Jari A Gida
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ’yan Najeriya mazauna ƙetare da su daina takaita gudummawarsu ga tura kuɗaɗe gida kawai, su mayar da hankali wajen zuba jari a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.
Tinubu ya yi kiran ne yayin buɗe taron tattalin arzikin ’yan Najeriya mazauna ƙetare na shekarar 2026 (NIDEC) a Toronto, Kanada, inda ya ce kuɗaɗen da suke turawa gida na taimaka wa jama’a wajen biyan kuɗin makaranta, magani da ƙananan sana’o’i.
Ya buƙaci ’yan Najeriya mazauna ƙetare su zuba jari a noma, kiwon lafiya, fasaha, makamashi, gidaje, sufuri, ma’adinai, ilimi da masana’antu, tare da haɗa jari wajen manyan ayyuka.
Shugaban ya ce gwamnati za ta samar da yanayi mai kyau da tsayayyun dokoki domin jawo masu zuba jari, tare da kare su daga damfara. Ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar ya samu ci gaba da kashi 3.89 cikin 100 a rubu’in farko na 2026.
Tinubu ya ƙara da cewa IMF ya yi hasashen tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da kashi 4.1 cikin 100 a shekarar 2026, yana mai cewa matakan gyaran tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar sun taimaka wajen inganta tattalin arzikin ƙasar.
#Tinubu #Najeriya #ZubaJari #YanNajeriyaMazaunaKetare #NIDEC2026 #TattalinArziki #IMF #Nigeria #Investment #DiasporaInvestment

Comments
Post a Comment