Tinubu ya gana da shugabannin APC 76 na Osun
Tinubu ya gana da shugabannin APC 76 na Osun
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da kusan shugabannin jam’iyyar APC 76 daga jihar Osun a fadar Aso Rock da ke Abuja, domin warware rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta.
Rahotanni sun ce taron ya biyo bayan wani rahoton bayanan sirri daga Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ya nuna cewa wasu shugabannin APC a Osun ba su gamsu da yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar ba, musamman yadda ake gudanar da yakin neman zaɓe.
A yayin taron, wasu shugabannin sun bayyana koke-kokensu kan yadda ake gudanar da harkokin jam’iyyar da kuma rabon nade-naden gwamnatin tarayya. Sun zargi sansanin tsohon gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola, da samun rinjaye a wasu nade-nade.
Shugaba Tinubu ya bukaci shugabannin su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su haɗa kai domin ganin ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu nasara a zaɓen. Ya kuma bayyana cewa rashin haɗin kan jam’iyyar na iya janyo mata asarar zaɓe.
#Tinubu #APC #OsunElection #Osun2026 #BolaOyebamiji #OsunAPC #NigeriaPolitics #AsoRock #NuhuRibadu #APCLeaders

Comments
Post a Comment