Trump Ya Musanta Rahotannin Ƙarancin Makamai a Amurka
Trump Ya Musanta Rahotannin Ƙarancin Makamai a Amurka
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake nanata cewa ƙasarsa ba ta fuskantar ƙarancin makamai. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, ya soki rahotannin da ke cewa makaman Amurka sun ragu, yana mai cewa ƙasar na da isassun makamai da harsasai.
Trump ya ce kamfanonin tsaro na Amurka na ci gaba da samar da makamai cikin sauri, tare da gina sabbin masana’antu da cibiyoyin kera makamai mafi yawa a tarihin ƙasar. Ya ƙara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da tura makamai zuwa duk inda ake buƙatarsu a lokacin da bukatar hakan ta taso.
Rahotanni sun nuna cewa a wani taron majalisar ministoci da aka gudanar a Camp David, Trump ya tambayi Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, bayani kan zargin ƙarancin harsasai. Jaridar Washington Post ta ce shugaban ya bayyana cewa yana tunanin an riga an magance matsalar.
Sai dai a sabon saƙonsa, Trump ya yi kakkausar suka ga waɗanda ya zarga da fitar da bayanan sirri, yana mai cewa an fara gurfanar da su a gaban shari’a, kuma za su iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa a gidan yari idan aka same su da laifi.
#Amurka #DonaldTrump #PeteHegseth #Makamai #Tsaro #LabaranDuniya #NexviewTV

Comments
Post a Comment