WAEC Ta Musanta Jerin Makarantu 50 Da Aka Ce An Riƙe Sakamakonsu Na WASSCE


 

WAEC Ta Musanta Jerin Makarantu 50 Da Aka Ce An Riƙe Sakamakonsu Na WASSCE


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Hukumar Shirya Jarabawar WAEC ta musanta wani jerin sunayen makarantu 50 da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka yi ikirarin cewa an riƙe sakamakon jarabawar WASSCE ta shekarar 2026. Hukumar ta bayyana cewa takardar ƙarya ce, domin an yi amfani da sunan Shugaban Ofishin WAEC na Najeriya, Dakta Amos Dangut, tare da tambari da hatimin da suka yi kama da na hukuma domin yaudarar jama’a.


Wannan bayani ya zo ne bayan WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta kwamfuta (CB-WASSCE) na shekarar 2026. Hukumar ta ce ta riƙe sakamakon ɗalibai 167,486, wanda ya kai kashi 8.59 cikin 100 na ɗalibai 1,950,726 da suka rubuta jarabawar, sakamakon zargin aikata maguɗin jarabawa.


WAEC ta bayyana cewa an riƙe sakamakon ne saboda laifuffuka daban-daban da suka haɗa da amfani da wayoyin hannu a ɗakunan jarabawa duk da haramcin hakan, da kuma shirya maguɗi a wasu makarantu. Haka kuma, hukumar ta ce an kama wasu masu sa ido da jami’an kula da jarabawa da ake zargi da taimakawa wajen aikata maguɗin jarabawa, kuma za a miƙa su ga ma’aikatun ilimi na jihohi domin ɗaukar matakin ladabtarwa.



#WAEC #WASSCE2026 #Jarabawa #Ilimi #ExamMalpractice #Najeriya #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill