WAEC Ta Tsawaita Wa’adin Rijistar GCE 2026 Zuwa 28 Ga Agusta
WAEC Ta Tsawaita Wa’adin Rijistar GCE 2026 Zuwa 28 Ga Agusta
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Jarabawa ta Yammacin Afirka, WAEC, ta tsawaita wa’adin rajistar jarabawar WASSCE ga masu zaman kansu ta shekarar 2026, kashi na biyu (Second Series).
WAEC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, inda ta ce yanzu za a ci gaba da karɓar rajistar har zuwa Juma’a, 28 ga Agusta 2026.
Hukumar ta buƙaci ɗalibai da sauran masu shirin rubuta jarabawar da su yi amfani da wannan ƙarin lokaci wajen kammala rajistarsu kafin wa’adin ya ƙare.
Jarabawar, wadda aka fi sani da WAEC GCE, an tanade ta ne musamman ga mutanen da ba sa cikin tsarin makarantun sakandare na yau da kullum. Hakan na ba wa waɗanda ke son samun takardar shaidar O’Level, ko kuma inganta sakamakon da suka samu a baya, damar sake rubuta jarabawar.
WAEC ta kuma bayyana cewa za a gudanar da jarabawar gaba ɗaya ne ta hanyar Computer-Based Examination (CBE). Kuɗin rajistar jarabawar ya kasance Naira 37,000, yayin da aka tsara gudanar da jarabawar tsakanin Satumba da Oktoba 2026.
Hukumar ta shawarci masu neman yin jarabawar da su je ofishin WAEC mafi kusa da su a jihar da suke domin tabbatar da garuruwan da za a gudanar da jarabawar, kafin su kammala rajistarsu.
#WAEC #WAECCGE2026 #WAECGCE #WASSCE2026 #Education #Exam2026 #NigeriaEducation #GCE #WAECNigeria #Students #OLevel #EducationNews

Comments
Post a Comment