Yan Bindiga Sun Kai Hari Katsina, Sun Kashe Mutane Biyu


 

’Yan Bindiga Sun Kai Hari Katsina, Sun Kashe Mutane Biyu

 

Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki Unguwar Aminu da ke Kandarawa, a Ƙaramar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina, inda suka kashe mutane biyu tare da raunata wasu huɗu.


Harin, wanda ya faru a daren Talata, 11 ga watan Agustan 2026, ya kuma yi sanadin sace mutane shida, uku daga cikinsu maza ne, yayin da sauran ukun mata ne.


Bayanai sun nuna cewa maharan sun tafi da dabbobi da dama, sannan suka shiga wasu shaguna suka kwashe kuɗi, wayoyin hannu da sauran kayayyaki.


An bayyana mutanen da suka rasa rayukansu a harin da Ibrahim Sama’ila da Mashakuru Isa. An gudanar da jana’izarsu tare da binne su a safiyar Laraba, bisa tsarin addinin Musulunci.


Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce sun hango ’yan bindigar tun suna kan hanyarsu daga Doma, da ke Ƙaramar Hukumar Faskari, amma daga baya suka ɓace kafin su sake bayyana a Unguwar Aminu.


Mafarauta da sauran jami’an tsaro sun yi yunƙurin tare musu hanya, amma maharan sun tsere daga yankin.


Bayan faruwar lamarin, mata da yara da dama sun fara barin garin zuwa wasu wurare domin neman mafaka, saboda fargabar sake kai musu hari.


Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya ce zai yi magana kan lamarin bayan ya tabbatar da abin da ya faru. Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga rundunar ba.


#Katsina #YanBindiga #Bakori #Tsaro #HareHare #Kandarawa #UnguwarAminu #SatarMutane #NigeriaSecurity #LabaranYau #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill